Najeriya

Wike ya bada tallafin naira miliyan 500 ga 'yan kasuwar Sokoto da gobara ta lakume

Gwamnan jihar Rivers a Najeriya Nyesom Wike
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya Nyesom Wike Daily Trsut

Gwamnatin Jihar Rivers dake Najeriya Nyesome Wike ya mika gudumawar naira miliyan 500 domin taimakawa 'yan kasuwar Jihar Sokoto da gobara ta kona ranar Talata. 

Talla

Wike wanda ya ziyarci Sokoto domin jajantawa gwamnatin Jihar da kuma Yan kasuwar, yace duk abinda ya taba Jihar Sokoto ya taba Jihar Rivers, saboda dangantakar dake tsakanin su, saboda haka zai zage damtse wajen ganin an sake gina kasuwar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da ya zaga da Wike kasuwar da ta kone, yace kashi 60 na shaguna 16,000 dake cikin ta sun kone kurmus.

Tuni Tambuwal ya nada kwamitin da zai gudanar da bincike da kuma bada shawara kan abında ya faru a kasuwar a karkashin mataimakin gwamnan Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.