Tattalin Arziki

Najeriya ta kashe kusan naira tiriliyan 2 kan sayen abinci a 2020

Tashar jiragen ruwa ta Apapa dake birnin Legas a Najeriya.
Tashar jiragen ruwa ta Apapa dake birnin Legas a Najeriya. REUTERS/Temilade Adelaja

Gwamnatin Najeriya tace kusan naira tiriliyan 2 ta kashe wajen sayen kayayyakin abinci daga ketare tsawon watanni 9, lokacin da dukkanin iyakokinta na kan tudu ke rufe.

Talla

Babban mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tattalin arziki Dakta Doyin Salami ne ya bayyana haka, a yayin da yake gabatar da jawabi ga taron masu ruwa da tsaki kan makomar tattalin arzikin kasar da ya gudana ta kafar bidiyo a birnin Legas.

A cewar dakta Salami duk da rufe iyakokin kan tudu da Najeriya tayi, saida gwamnati ta kashe naira tiriliyan 1 da biliyan 850 wajen shigar da kayayyakin abinci cikin kasar a tsakanin watan Janairu zuwa Satumban shekarar 2020, karin akalla kashi 60 idan aka kwatanta da kudin da aka kashe a 2019.

Mai baiwa gwamnatin Najeriyar shawara kan tattalin arzikin ya kara da cewar, makudan kudaden da suka kashe wajen sayen abincin daga kasashen ketare, ya nuna cewar har yanzu kasar ba za ta iya ciyar da kanta ba, dan haka ya zama dole a sake yiwa tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki garambawul.

Dakta Salami ya ce akalla manoma miliyan 2 da dubu 500 ne suka tafka hasarar amfanin gonar da suka noma sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa a shekarar 2019.

Wani rahoton hukumar kididdigar Najeriya ta fitar a watan Mayun shekarar bara, ya nuna cewar a 2019, naira tiriliyan 40.21 aka kashe kan kyayyakin abinci da sauran bukatu a Najeriya, sabanin naira tiriliyan 21.62 a shekarar 2018, abinda ke nuni da karuwar farashin kayayyakin abincikin akai akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.