Najeriya

Sama da 'yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba bayan ganawa da Shiekh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi YouTube

Rahotanni daga jihar Kaduna sun ce sama da ‘yan bindiga 500 ake sa ran za su tuba tare da ajiye makamansu, biyo bayan tattaunawa da fitaccen malamin addinin Musulunci Shiekh Ahmad Gumi a baya bayan nan.

Talla

Jaridar Desert Herald dake kan shafin internet a Najeriya ta ruwaito cewar ‘yan bindigar da ake sa ran za su tuba sune wadanda suka addabi babbar hanyar Zaria zuwa Giwa, da kuma karamar hukumar birnin Gwari.

Yayin taron wa’azin an baiwa jagororin ‘yan bindigar damar jawabi, inda bayanai suka nuna kusan dukkaninsu baki yazo daya wajen bayyana dalilan da suka tilasta musu daukar makamai, wadanda suka hada da cin zarafin da ake musu, kyara, kame su da jami’an tsaro ke yi ba bisa hakki ba tare da karbe musu kudade, sai kuma kisan gillar da wasu bata-garin jami’an tsaron ke musu.

A makwannin da suka gabata ne dai rahotanni suka ce Shiekh Ahmad Gumi yayi tattaki zuwa yankin Sabon Garin Yadi dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna, inda ya gabatar da wa’azi ga mazauna yankin, inda Fulani da dama ke zaune.

Bayanai sun nuna cewar yunkurin Shaihin malamin na tunkarar warware matsalar ‘yan bindiga ta hanyar tattaunawa ya samu goyon bayan gwamnatin Najeriya da kuma hukumomin tsaron kasar, kamar yadda Jaridar Desert Herald ta ruwaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.