Najeriya

Doka ta baiwa 'yan Najeriya damar zama a duk inda suka so - Dattawan Arewa

Tambarin kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ACF
Tambarin kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ACF Credit: Channelstv

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bayyana cewar babu wani mahaluki dake da hurumin korar wani dań kasa dake zama a wani yanki saboda kariyar da kundin tsarin mulki ya bashi.

Talla

Wannan ya biyo bayan umurnin da Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya baiwa Fulani makiyaya ake dazukan Jihar da su fire cikin mako guda ko kuma su gamu da fushin hukuma.

Mai magana da yawun kungiyar ta ACF Emmanuel Yawe yace kundin tsarin mulkin da Najeriya ke amfani da shi ya baiwa kowanne ‘dan kasa damar zama inda yake so, inda yake cewa idan wani Bafulatani ya aikata laifi a Jihar Ondo, aikin hukuma ce ta kama shi domin hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar tace ko wanne irin laifi na dauke da hukunci, saboda haka kungiyar bata ga wata dokar da ta hana wani ‘dań kasa zama a kowanne bangare ba, domin gudanar da hakkokin są kamar yadda doka ta tanada.

Jami’in yace su kansu Fulani makiyayan dake Jihar Ondo na fuskantar ta’addancin hare hare da garkuwa da su domin karbar kudin fansą, yayin da ake sace shannun su, saboda haka suna bukatar kariya.

Kungiyar dattawan Arwacin Najeriyar tace abında take bukata daga wurin Gwamnan Ondo wanda tsohon shugaban lauyoyin Najeriya ne, shi ne hukunta masu laifi daga cikin su, amma ba umurnin korarsu daga jihar baki daya ba.

A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamna Rotimi ya gabatar da wannan umurni, wanda ya gamu da suka daga fadar shugaban kasa da kuma kungiyoyi daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.