Najeriya

Gwamnati ta kaddamar shirin gina gidaje dubu 300 a sassan Najeriya

Wasu daga cikin ire-iren gidajen da gwamnati ke ginawa a Najeriya.
Wasu daga cikin ire-iren gidajen da gwamnati ke ginawa a Najeriya. Daily Trust

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da gine-ginen gidaje akalla dubu 300, da nufin taimakawa kananan ma’aikata da sauran masu karamin karfi.

Talla

Shirin gine-ginen dai zai lashe naira biliyan 200, wanda kuma zai samar da aikin yi ga kusan mutane miliyan 1 ad dubu 800.

Sai dai kwararru na nuna damuwa kan matsalar rashin ingancin gine-ginen, wadanda a wasu lokutan suke rushewa tare da salwantar da rayuka.

Wakilinmu na Abuja Mohammed Sani Abubakar hada mana rahoto.

Rahoto kan shirin gwamnatin Najeriya na gina gidaje dubu 300 a fadin kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.