Najeriya

Kotun Najeriya ta mallakawa gwamnati kudaden tsohon Gwamnan Zamfara

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari
Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari RFI Hausa

Wata Kotu da ke Abuja babban birnin Najeriya ta bada umurnin mallakawa gwamnati wasu makudan kudade mallakar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da aka gano su a bankunan Zenith da Polaris.

Talla

Mai shari’a ta kotun Ijeoma Ojukwu ta ce tsohon gwamnan ya gaza wajen hana daukar matakin kamar yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bukata.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ce kudaden da aka ajje su a asusu daban daban sun hada da Dala dubu 56,056 a Bankin Polaris da naira miliyan 12 da dubu 900 da wasu naira miliyant 11 da dubu 200 da kuma Dala dubu 301,319 da naira dubu 217,388 da kuma wasu naira miliyan 311,872.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.