Najeriya

Shekau ya fitar da sabon sako

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau.
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau. AFP PHOTO / BOKO HARAM

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya ftar sabon sakon murya inda ya bukaci sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su tuba, gami da gargadinsu da cewar ba za su iya yin kokari sama da na wadanda suka maye gurbinsu ba.

Talla

A sautin da ya fitar mai tsawon mintuna tara da dakika 56, da Jaridar Humangle.ng ta ruwaito, Shekau ya ce ya samu labarin yi wa tsoffin manyan hafsoshin tsaron Najeriya murabus da maye gurbinsu da sabbi, inda ya bukaci sabbin da su tuba su amshi musulunci.

A cikin sabon sautin muryar jagoran na Boko Haram ya ambaci sunayen manyan hafsohin tsaron daya bayan daya gami da ikirarin cewar ba za su iya tarwatsa kungiyarsa ba.

Sako na karshe kafin na baya bayan nan da Shekau ya fitar dai shi ne wanda yayi ikirarin mayakansa ne suka sace dalibai sama da 300 na makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara dake jihar Katsina, ikirarin da hukumomin Najeriya ta karyata tare da tabbatar da cewar ‘yan bindiga ne suka sace daliban da aka yi nasarar kubutar dasu baki daya, amma ba Boko Haram ba.

Ranar Talatar da ta gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da yi wa tsoffin manyan hafsoshin tsaron murabus tare da maye gurbinsu da sabbi, da suka hada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin Hafsan Hafsoshin tsaro, Manjo Janar Ibrahim Attahiru shugaban sojin kasa, sai kuma Rear Admiral A.Z. Gambo a matsayin shugaban sojin ruwa tare da Air Marshall I.O Amao a matsayin shugaban sojin sama.

Kungiyoyi da mutane da dama dai sun dade suna kira ga shugaban Najeriyar da ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar, ganin yadda matsalolin tsaro suka ki ci suka ki cinyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.