Wasanni

Bazan gayyaci sabbin 'yan wasa ba - Rohr

Cocin Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr
Cocin Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr REUTERS/Heinz-Peter Bader

Kocin Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr ya ce babu wani sabon dan wasa da zai gayyata don wasan neman tikitin shiga gasar cin Kofin Afirka na 2021 da tawagar za ta kara da jamhuriyar Benin da kuma Lesotho.

Talla

Da yake hira da manema labararai kuma a ka watsa a shafin YouTube na kungiyar, bayan dawowarsa Najeriya ranar Litinin, Rohr ya karyata rahotannin kafofin yada labarai na cewa FIFA ta baiwa wasu sabbin ‘yan wasa izinin buga wa Najeriya kwallo.

Kocin dan kasar Fransa da Jamus ya dage kan cewa yana da kwararrun 'yan wasa a hannun sa kuma ba zai yi tunanin kawo wani sabon dan wasa ba a yanzu, yayin da' yan wasan ke shirin wasan karshe na wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2021.

Super Eagles, wadanda ke saman teburin rukunin L da maki takwas a wasanni hudu, za ta kara da Benin a waje ranar 22 ga watan Maris, kafin ta karbi bakuncin Lesotho 30 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI