Najeriya

'Yan Najeriya basa bukatar izinin zama dazukan Ondo - Bala Mohammed

Gwamnan JIhar Bauchi a Najeriya Sanata Bala Muhammad.
Gwamnan JIhar Bauchi a Najeriya Sanata Bala Muhammad. RFI Hausa / Shehu Saulawa

Gwamnan Jihar Bauchi dake Najeriya Bala Muhammed ya ce 'Yan Najeriya basa bukatar izini daga Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu domin zama a cikin dazukan Jihar ko kuma wani bangare na Najeriya.

Talla

Muhammed dake mayar da martani kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya da su fice daga dazukan Jihar sa, yace umurnin kuskure ne, domin kuskure ne a bayyana daukacin Yan kabila guda a matsayin masu aikata laifi sakamakon ayyukan wasu yan kalilan daga cikin su.

Gwamnan Bauchin yace kundin tsarin mulki ya baiwa gwamnatocin jihohi da tarayya amanar kula da filaye a madadin jama’a, amma yan kasa basa bukatar izinin gwamnoni ko gwamnatin tarayya wajen zama a wani yanki.

Muhammed yace sashe na 41 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa yan kasa damar zama a duk inda suke so bisa ka’idar doka.

Dangane da mallakar bindiga, Gwamnan Ondo Rotimi Akeredolu ya zargi takwaran sa na Bauchi da tinzira jama’a su mallaki makamai sabanin abinda dokar kasa ta tanada, kamar yadda kwamishinan yada labaran sa Donald Ojogo ya shaidawa manema labarai, inda yake cewa kuskure wadannan kalamai.

Gwamna Akeredolu ya bayyana kalaman Gwamnan Bauchi a matsayin wadanda ke iya jefa Najeriya cikin tashin hankali muddin aka goyi bayan Fulani makiyaya su mallaki bindiga, yayin da sauran jama’a kuma zasu zauna haka hannu banza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI