Najeriya

Atiku ya goyi bayan sayar da kadarorin Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar (AP Photo/Manuel Balce Ceneta)

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya goyi bayan shawarar Gwamnatin Tarayya na sayarda wasu kadarorin ta.

Talla

Kadarorin da gwamnati ta nuna sha’awar mallakawa ‘yan kasuwa masu zaman kansu, sun hada da matatun man kasar da Babban dakin taro na kasa-da-kasa dake Abuja da kuma filin taron Tafawa Balewa dake Lagos, da Kamfanonin samar da wutar lantarkin Yola, da Zungeru, da dai sauransu.

Ana sa ran gwamnati ta samu jimlar kudi har sama da Naira biliyan 493 daga kadarorin wanda aka karkasasu zuwa sashe -sashe da suka hada da na makamashi da na masana'antu da sashen sadarwa, da cibiyoyin ci gaba da kuma albarkatun kasa.

A cikin wata sanarwa da Atiku Abubakar ya fitar mai taken ‘sayar da Matatun Man Fetur da Sauran Kadarorin, tsohon shugaban kasar wanda ya taba jagorantar saida kaddarorin gwamnati a zamanin mulkinsu, ya yi kira da a nuna gaskiya wajen aiwatar da Shirin.

Atiku ya bayyana farin cikin sa dangane da wannan shiri na gwamnati da yayi yakin neman zaben sa akai, to said ai kuma jam’iyyar Apc ta caccaki matakin abaya, sai kuma gashi ta bi sahun manufofin madugun adawar na siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI