Najeriya

Najeriya: Boko Haram sun yi wa 'yan gudun hijira 5 yankan rago a Barno

Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram.
Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram. AFP PHOTO / BOKO HARAM

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla 'yan gudun hijira 5 ne mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a karamar hukumar Damboa da ke Jihar Barno lokacin da suka je yin itace a daji, yayin da wasu kuma suka bace.

Talla

Wani jami’i a kungiyar 'yan sa kai Abu Damboa ya shaida wa Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya cewar 'yan gudun hijirar sun bata ne lokacin da suka je yin itace jiya Lahadi.

Abu Damboa ya ce wannan ya sa suka fita neman su a cikin dajin, inda suka samu gawarwakin 5 daga cikinsu bayan an fille kansu, kilomita biyu daga inda suke saran itacen.

Hukumomin agaji sun tabbatar da lamarin, yayin da suka ce yau Litinin an yi wa mutanen jana’iza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI