Najeriya

Hare-hare sun hallaka 'yan Najeriya dubu 4 da 556 a 2020- Global Right

Gawarwakin wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a Zamfara
Gawarwakin wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a Zamfara RFI

Wai Bincike da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Duniya da ake kira Global Rights ta gudanar ya bayyana yadda munanan hare hare a sassan Najeriya ya hallaka mutane dubu 4 da 556 cikin shekarar 2020.

Talla

Rahotan kungiyar da ya kunshi harin ta’addanci da fada tsakanin kabilu a yankunan kasar da kuma hare hare, kisan gilla baya ga garkuwa da mutane, ya kuma nuna yadda aka samu karuwar mutanen da ke rasa rayukansu idan aka kwatanta da alkaluman shekarar 2019 da akalla mutum dubu 1 da 368.

Global Rights ta ce Najeriya na ci gaba da fuskantar munanan hare hare ta fuska biyu da suka shafi tsaro da suka hada da ayyukan ta’addanci da kuma na 'yan bindiga, baya ga wasu matsalolin da suka dabaibaye ta da suka hada da talauci da almubazzaranci da dukiyar kasa da rashin ayyukan yi, sai kuma illar da annobar coronavirus ta haifar.

Kungiyar ta ce alkaluman da ta tattara sun nuna adadin rayukan da suka salwanta bara zuwa dubu 4 da 556, sabanin dubu 3 da 188 na shekarar 2019, kuma daga cikin wannan adadi dubu 3 da 858 fararen hula ne, yayin da 698 kuma jami’an tsaro ne.

Jihohin da suka fi fuskantar azabar kashe kashen su ne Borno ma mutane 1,176 sai Kaduna mai 628, Katsina mai 501, Zamfara 262 sannan Niger mai 254.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI