Najeriya-Coronavirus

Najeriya ta gano sabon nau'in Coronavirus a Lagos

Bayanai sun ce Najeriya ta gano nau'in cutar tun cikin watan Nuwamban da ya gabata.
Bayanai sun ce Najeriya ta gano nau'in cutar tun cikin watan Nuwamban da ya gabata. NEXU Science Communication/via REUTERS

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya ta sanar da gano wani sabon nau’in coronavirus sabanin wanda aka saba gani a cikin shekara guda da ta gabata.

Talla

Shugaban hukumar Chikwe Iheakwazu ya bayyana sabon nau’in a matsayin B.1525 kuma an same shi ne daga cikin gwajin da aka yiwa wani mutum a ranar 23 ga watan Nuwamba bara a birnin Lagos.

Jami’in ya ce wannan sabon nau’in da aka samu a wasu kasashe baya cikin wadanda aka bayyana a matsayin masu matukar illa, kuma yanzu haka an same shi a jihohin Najeriya guda 5.

Shugaban hukumar ya ce masu binciken kimiya na aiki tukuru domin gano ko wannan nau’in na da illa wajen yaduwar sa da kuma kan garkuwar jiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI