Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace daliban Sakandiren 'yammata ta Jangebe a Zamfara

'Yan bindiga a Arewacin Najeriya na ci gaba da cin karensu babu babbaka duk da ikirarin gwamnati na yaki da su.
'Yan bindiga a Arewacin Najeriya na ci gaba da cin karensu babu babbaka duk da ikirarin gwamnati na yaki da su. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Rahotanni daga Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kai farmaki kan makarantar ‘yan mata da ke Jangebe a Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da dalibai, wadanda kawo yanzu babu karin bayani kan adadinsu.

Talla

Wata majiya ta shaidawa sashen Hausa na RFI cewar adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ya kai 300.

Lamarin na zuwa ne yayin da hukumomin Najeriyar ke cigaba da kokarin kubutar da daliban makarantar sakandaren Kagara 27 baya ga ma'aikata da kuma malamansu 15 da wasu ‘yan binidgar suka sace a Jihar Neja.

A shekarar bara wasu gungun ‘yan binidgar suka sace dalibai sama da 200 daga makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara da ke jihar Katsina, wadanda aka sako su bayan shafe kusan mako guda ana garkuwa da su.

Hare-haren ‘yan binidga da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da yin kamari a baya bayan nan, duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan kawo karshen matsalar da suka hada da murkushe barayin da karfin jami’an tsaro, tare da mika musu tayin sulhu a matakan wasu jihohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI