Najeriya - Zamfara

Daliban Jengebe 7 sun sulale daga hannun 'yan bindiga

Sojojin Najeriya dake ayyukan samar da zaman lafiya
Sojojin Najeriya dake ayyukan samar da zaman lafiya AFP - -

A Najeriya, rahotanni daga Zamfara sun ce 7 daga cikin dalibai mata 317 da ‘yan binidga suka sace daga makarantar ‘yammata ta Jengebe sun koma gida.

Talla

Wata majiya da ta tabbatar da kubutar ‘yammatan 7, tace daliban sun samu nasarar sulalewa daga hannun ‘yan binidigar ne, a yayin da suke tafiya cikin daji.

Yanzu haka dai hadin gwiwar jami’an tsaro sun shiga farautar ‘yan bindigar da zummar ceto sauran daliban da aka yi garkuwa dasu, kamar yadda rundunar ‘yan  sandan jihar Zamfara ta tabbatar.

Hare-haren ‘yan binidga da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da yin kamari a baya bayan nan, duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan kawo karshen matsalar da suka hada da murkushe barayin da karfin jami’an tsaro, tare da mika musu tayin sulhu a matakan wasu jihohi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI