Najeriya-Kano

Mashawarcin Ganduje ya rasa aikinsa saboda caccakar gwamnati

Tsohon mashawarcin gwamnan Kano kan kafafen labarai Salihu Tanko Yakasai daga bangaren hagu, tare da mahaifinsa Alhaji Tanko Yakasai, da kuma wani dan uwansa daga bangaren dama.
Tsohon mashawarcin gwamnan Kano kan kafafen labarai Salihu Tanko Yakasai daga bangaren hagu, tare da mahaifinsa Alhaji Tanko Yakasai, da kuma wani dan uwansa daga bangaren dama. © Twitter / Peacock @dawisu

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kori mai bashi shawara kan kafafen yada labarai Salihu Tanko Yakasai saboda caccakar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC a dukkanin matakai da yayi.

Talla

Kwamishinan yada labaran jihar Kano Muhammad Garba yace matakin na korar Salihu Tanko Yakasai ya soma aiki nan take, inda ya kara da cewar tsohon mai bada shawarar ya gaza tantance banbancin ra’ayin kashin kai da kuma matsayin hukuma kan lamurran da suka shafi al’umma, dan haka babu bukatar jami’in ya cigaba da aiki a karkashin gwamnatin da bai yadda da ita ba.

Matakin gwamna Ganduje na korar Salihu Tanko Yakasai na zuwa ne a yayin da iyalansa da sauran ‘yan uwa da abokan arziki ke cigaba da laluben inda ya shiga, bayan da aka neme shi aka rasa sa’o’i bayan caccakar da ya yiwa shugaban Najeriya da kuma jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

A Juma’ar da ta gabata, yayin bayyana bacin ransa kan sace daliban makarantar Jangebe sama da 300 da ‘yan bindiga suka yi ta shafinsa na twitter, Salihu Tanko Yakasai ya caccaki shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da cewar sun gaza cika alkawuran da suka daukar wa ‘yan Najeriya a dukkanin matakai.

Tuni dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta musanta rahotannin dake cewa jami’an ta ne suka yi awon gaba da tsohon mai bada shawarar ga gwamnatin Kano.

A nashi bangaren, yayin karin bayan kan abinda ya sani dangane da batan dan sa, daya daga cikin dattawan Arewacin Najeriya Alhaji Tanko Yakasai, ya ce an yi awon gaba da Salihu ne a yayin da bar gida da yammacin ranar Juma’a da zummar zuwa aski, wanda kuma har yanzu aka gaza gano inda yake.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.