Najeriya

Gungun 'yan bindiga sun sake kai farmaki kan garin Kagara dake Neja

Allon makarantar sakandaren garin Kagara dake jihar Neja da 'yan bindiga suka sake kaiwa farmaki.
Allon makarantar sakandaren garin Kagara dake jihar Neja da 'yan bindiga suka sake kaiwa farmaki. AP

Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutane akalla 4, yayin sabon farmaki da suka kai kan garin Kagara.

Talla

Wasu da suka tsira daga farmakin sun shaidawa jaridar Daily Trust dake Najeriya cewar, akalla mutane 11 ‘yan bindigar suka sace tare ta kore dabbobi da dama daga kauyukan Rubo da Karako, a sabon farmakin da suka kai kan garin na Kagara.

An dai kai farmakin na baya bayan nan ne sa’o’i bayan sakin daliban makarantar sakandaren garin na Kagara 27 da malamansu da wasu ma’aikata 15 da ‘yan binidiga suka yi a yau Asabar, bayan da suka shafe kwanaki 10 suna garkuwa da su.

Garin Kagara dake Neja ya dade yana fuskantar har-haren ‘yan bindiga dake garkuwa da mutane da kuma satar dabbobi.

Hare-haren ‘yan binidga da satar mutane a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da yin kamari a baya bayan nan, duk da ikirarin gwamnati na daukar matakan kawo karshen matsalar da suka hada da murkushe barayin da karfin jami’an tsaro, tare da mika musu tayin sulhu a matakan wasu jihohi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI