Najeriya - Coronavirus

Najeriya zata karbi kason farko na alluran rigakafin korona ranar Talata

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta karɓi kason farko na alluran rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca ranar Talata.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta karɓi kason farko na alluran rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca ranar Talata. THOMAS KIENZLE AFP/File

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta karɓi kason farko na alluran rigakafin korona ta Oxford-AstraZeneca har miliyan hudu ranar Talata.

Talla

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban, Kwamitin Shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19, Boss Mustapha, ya bayyana hakan cikin wani sakon bidiyo da aka gabatar wa manema labarai.

Ya ce Najeriya za ta karɓi rigakafin ne ƙarƙashin shirin hukumar lafiya ta duniya WHO da ake kira COVAX na rarraba rigakafin ga ƙasashen duniya.

Gwamnatin, wacce a baya ta sanar da cewa alluran rigakafin za su isa kasar nan da karshen watan Fabrairu, daga bisani ta ce mai yiwuwa a cikin makon farko na watan Maris.

Amma a sakonsa na baya-bayan nan, Sakataren na Gwamnatin Tarayya ya ce: “ya tabbatar da cewa alluran rigakafin na kan hanya kuma zasu iso cikin gaggawa.

“Mun yi imanin cewa allurar rigakafinmu za su tashi daga Indiya a ranar 1 ga watan Maris, na wannnan shekara ta 2021 da misalin karfe 10:30 na dare kuma su isa Abuja a ranar 2 ga watan Maris da 11:10 na safe, Kuma muna shirye-shiryen akai”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.