Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta kashe mutane a Dikwa

Shugaban Boko Haram Abubakar shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar shekau AP - TEL

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar kungiyoyin agajin da ke aiki a jihar Borno ta Najeriya sun shaida mata cewar fararen hula 6 aka kashe a kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai Dikwa a ranar Litinin

Talla

Sanarwar da kungiyoyin 54 suka gabatar, ta ce akalla fararen hula guda 6 suka mutu lokacin da aka yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da mayakan Boko Haram, yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan wadanda suka bace.

Kakakin Kungiyar Agaji ta Red Cross a Najeriya ya ce sun karbi mutane 6 da suka samu raunuka domin kula da su bayan harin na Dikwa, daya daga cikin garuruwan da ake da tarin masu aikin agaji.

Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon ya ce mayakan sun kai harin ne kai tsaye kan cibiyoyin kungiyoyin agaji abin da ya shafi aikin taimaka wa mutane kusan dunu 100,000 da ke bukatar taimako.

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana samun nasarar dakile harin wanda ke zuwa kwanaki bayan kakkabe mayakan Boko Haram daga Dikwa da kauyukan dake kusa da garin.

Daraktan yada labaran sojin Janar Mohammed Yarima ya ce mayakan sun kai harin ne da tarin makamai da kuma motocin da ke dauke da manyan bindigogi amma kuma jami’ansu sun yi nasarar dakile harin.

EMBED: Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya bada tallafin abinci ga mutane dubu 34 a Dikwa

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ruwaito wasu majiyoyi na cewa mayakan sun yi nasarar kwace iko da garin na wani lokaci tsakanin Litinin zuwa Talata kafin sojoji su kore su.

Garin Dikwa na dauke da mutane akalla 114,000 ciki har da 'yan gudun hijira 75,470 da suka tsere daga garuruwansu domin kaucewa hare-haren Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.