Najeriya

Tattaunawa da Sale Jigo Shugaban gundumar Gidan Runji kan ‘yan gudun hijira

Akwai kimanin 'yan gudun hijira dubu 70 da ke rayuwa a sansanin Gamborou
Akwai kimanin 'yan gudun hijira dubu 70 da ke rayuwa a sansanin Gamborou AFP

Sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da tsananta a Najeriya ‘yan gudun hijira kimanin dubu bakwai ne yanzu haka suka tsere zuwa jihar Maradi ta Jamhuriya Nijar, musaman Gundumar Gidan Runji da ke iyaka da Jihohin Sokoto da Zamfara, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta majalisar Dinkin Duniya.

Talla

Shugaban gundumar Gidan Runji,  Malam Sale Jigo ya ce adadin ya zarta yadda ake cewa, sai dai ya koka da rashin kokarin magabatan Nigeria wajen yakar wadannan 'yan ta’dda, lura da cewa akwai garuruwan Nigeria da mutanensu ke zuwa Niger su kwana saboda sun fi samun tsaro.

Dangane da wannan Salisu Isa ya tattauna da shugaban gundumar ta gidan Runji Malam Sale Jigo kan halin da 'yan gudun hijirar ta Najeriya ke ciki yanzu haka a Nijar ga kuma yadda zantawarsu ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.