Najeriya-UNICEF

UNICEF ta yi tir da farmakar makarantu a Najeriya bayan sakin daliban Jangebe

Daliban Sakandiren Jangebe bayan kubutar da su daga hannun 'yan bindiga a Jihar Zamfara.
Daliban Sakandiren Jangebe bayan kubutar da su daga hannun 'yan bindiga a Jihar Zamfara. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta bayyana farin cikin kubutar da daliban makarantar Sakandaren 'yammata ta Jangebe 270 wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara da ke Najeriya a makon jiya.

Talla

Sanarwar ta UNICEF mai dauke da sanya hannun Olumide Akintunde ta ce yayinda su ke murnar kubutar da daliban mata, suna kuma jaddada matsayin su cewar kai hari kan makarantu ko dalibai ya sabawa ‘yancin yara na samun ilimi.

UNICEF ta bukaci hukumomin Najeriya da su dauki duk matakan da suka dace na kare makarantu domin bai wa yara damar samun ilimi ba tare da fargaba ba.

UNICEF ta ce za ta hada kai da ma’aikatar ilimi domin taimakawa wadannan dalibai wajen karfafa musu gwiwar komawa makaranta domin cigaba da karatun su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.