Najeriya-'Yan sanda

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Calabar

Wasu Jami'an 'yan sandan Najeriya da ke kokarin kwantar da tarzomar matasa
Wasu Jami'an 'yan sandan Najeriya da ke kokarin kwantar da tarzomar matasa AFP/File

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun kai hari cibiyoyin 'yan sanda guda biyu da ke Calabar, inda suka kashe jami’ai guda 6 da kuma kwashe makamansu.

Talla

Rahotanni sun ce, 'yan bindigar da ke rera wakar 'yan aware ta IPOB sun fara kai hari ne wajen binciken ababan hawa da ke karamar Hukumar Obubra, inda suka kashe 'yan Sanda guda biyu, yayin da wasu kuma suka kai hari a Oyadama, inda suka kashe 'yan sandan guda 4.

Bayani sun ce, 'yan bindigar sun kuma harbi wani soja a hannu amma bai mutu ba.

Hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da yaduwa a sassan Najeriya sakamakon samun karuwar makamai a hannun jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.