Ana neman yi mana rinto kan aikin gina tashar lantarki ta Mambila - Gwamnoni
Wallafawa ranar:
Gwamnaonin jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewar aikin gina tashar samar da wutar lantarkin Mambila da gwamnatin tarayya tace tana yi, yana kunshe ne kawai a cikin takardu domin babu abinda ke gudana a zahiri.
Sanarwar bayan taron da Gwamnonin suka gabatar a Bauchi ta bukaci gwamnatin tarayya da ta baiwa aikin muhimmancin da ya dace kamar yadda take gudanar da manyan ayyuka a wasu sassan kasar, saboda muhimmancin sa ga yankin da kuma jama’a baki daya.
Sanarwar dake dauke da sanya hannu Gwamnan Barno Babagana Umara Zulum ta kuma koka kan irin kudaden manyan ayyuka da gwamnatin tarayya ta warewa yankin nasu a kasafin kudin bana.
Gwamnonin sun bayyana shiri na musamman kan bunkasa harkar bada ilimi wajen kafa hukumar shiya da zata dinga sanya ido da kuma bada gudumawa akai, yayin da suka yabawa gwamnatin tarayya na zabo wasu hanyoyin yankin domin baiwa kamfanin Dangote aikin gina su, tare da kamfanin Lafarge/Ashaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu