Najeriya-Afrika ta Kudu

Kamfanin FilmOne zai yi tallan shirin 'Coming To America' na 2 a Najeriya

Eddie Murphy, jagoran taurarin shirin fim din 'Coming to America' kashi na 1 da na 2 tare da mai taimaka masa Arsenio Hall.
Eddie Murphy, jagoran taurarin shirin fim din 'Coming to America' kashi na 1 da na 2 tare da mai taimaka masa Arsenio Hall. AP - Quantrell D. Colbert

Kamfanin FilmOne ya bayyana shirin gabatar da wani sabon Fim da aka yiwa suna ‘Coming To America’ kashi na 2 a gidajen siniman Najeriya daga gobe juma’a 5 ga watan Maris.

Talla

Shi dai wannan shirin da za’a gabatar ta hanyar kamfanin Amazon Prime ga kasashen duniya, za a gabatar da shi ta gidajen sinima ne kawai a kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu.

Taurarin fina-finai KiKi Layne, daga hagu tare da Eddie Murphy a cikin shirin fim din 'Coming to America' kashi na 2 da za a haska.
Taurarin fina-finai KiKi Layne, daga hagu tare da Eddie Murphy a cikin shirin fim din 'Coming to America' kashi na 2 da za a haska. AP - Quantrell D. Colbert

Shirin da aka fara gabatar da shi shekaru 30 da suka gabata na dauke da tauraron fina-finai Eddie Murphy wanda ya fito daga Masarautar Zumunda lokacin da ya bar kasar su zuwa Amurka.

Ginshikin labarin ‘Coming To America’

A shirin farko da aka yi shekaru 31 da suka gabata, Murphy na yin watsi da rayuwar gidan Sarautar da ya fito domin samun budurwa wadda bata fahimci irin gidan da ya fito ba.

Wani bangaren ban dariya a shirin fim din 'Coming to America' kashi na 2.
Wani bangaren ban dariya a shirin fim din 'Coming to America' kashi na 2. AP - Quantrell D. Colbert

Bayanai sun ce akasarin mutanen da suka shiga shirin na farko sun sake taka rawa a sabon shirin da za a gabatar gobe.

Shekaru 30 da suka gabata dai shirin fim din na 'Coming to America' kashi na 1 ya samu karbuwa ga dimbin masoya kallon fina-finai a sassan duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.