Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya 101 sun bace bayan harin Boko Haram

Wasu daga cikin sojojin Najeriya masu yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wasu daga cikin sojojin Najeriya masu yaki da Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar. AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla sojoji 101 suka bata bayan kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai garuruwan Marte da Dikwa da ke Jihar Barno.

Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar daga sojojin da suka bata akwai hafsoshi 12 da kuma kananan sojoji 86 kamar yadda wasikar da Kanar A.O. Odubuyi ya rubuta a madadin Kwamandan rundunar dake yaki da boko haram ta Lafiya Dole dake Maiduguri.

Wasikar tace daga cikin sojojin akwai masu rike da mukamin Manjo guda 3 da Kaftin guda 3 da laftanar guda 6 da Saje-Saje guda 3 da kuma kananan sojoji 89.

Wasikar ta bayyana wadannan jami’ai a matsayin wadanda suka gudu daga wurin aiki lokacin da mayakan boko haram suka kai hari a Sabuwar Marte da Dikwa.

Wasikar sojin ta bukaci bayyana wadannan dakaru a matsayin wadanda suka gudu daga aiki, yayin da ta bada umurnin rufe asusun ajiyar su da kuma kamo su ko yi musu rakiya zuwa Cibiyar sojin duk inda aka gan su.

Jaridar tace Daraktan yada labaran sojin Janar Mohammed Yerima bai yi karin haske game da labarin ba, inda yake cewa idan suna da bayanin da ya dace duniya ta sani za suyi Magana akai.

A ranar 14 ga watan Fabarairu mayakan boko haram suka kai hari Marte inda suka karbe iko da garin kafin kai hari Dikwa ranar 19 ga wata, abinda ya sa shugaban sojin Janar Attahiru Ibrahim ya ziyarci dakarun inda ya basu umurnin sake kwato garin da kauyukan dake kusa da shi.

Ziyarar shugaban sojin ya karfafawa sojin gwuiwar sake kwace iko da Marte da wasu garuruwa dake yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.