Najeriya-Boko Haram

Tubabbun Boko Haram sun koma gidan jiya-Zulum

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP

Gwamnan jihar Borno da ke Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar wasu daga cikin mayakan Boko Haram da suka aje makamansu, aka kuma horar da su wajen sauya tinaninsu  sun koma gidan-jiya, inda suka sake daukar makamai.

Talla

Saboda haka Zulum ya bukaci soke shirin da kuma bai wa gwamnatin Najeriya shawarar gurfanar da daukacin wadanda aka kama da zargin shiga ayyukan ta’addanci domin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 11 ana fafatawa ba tare da kammala shi ba.

Yayin gudanar da taron Kungiyar Gwamnonin da suka fito daga Jihohin Arewa Maso Gabas, Zulum ya bayyana takaicinsa da wannan mataki, inda ya bayyana cewar mayakan Boko Haram na sake dabaru da kuma kai munanan hare-hare.

Gwamnan ya ce tabbas shaidu sun nuna cewar shirin horar da mayakan da suka tuba domin sauya tinaninsu ko kuma ba su damar aje makamai ba ya aiki, ganin yadda a lokaci da dama wadannan mutane da aka horar sun koma sun dauki makamai domin ci gaba da kai hare-hare.

Zulum ya ce horan da tubabbun ke samu na ba su damar fahimtar yadda ake gudanar da harkokin tsaro a yankunan da suke da kuma kai musu hari, yayin da al’ummomi da dama  ba sa bukatar sake karbar irin wadannan mutane saboda fargaba da kuma kallon su a matsayin wadanda suka aikata mummunar laifi a kansu.

Saboda haka Gwamnan ya ce babu dalilin ci gaba da aiwatar da irin wannan shirin kamar yadda ake gudanarwa yanzu, ba tare da sake nazari akan sa ba da kuma nasarar da ake so ya cimma.

Zulum ya ce mafita kawai ita ce yi wa irin wadannan mutane shari’a bisa dokar yaki da ta’addanci, yayin da wadanda aka tilastawa shiga kungiyar kawai za a basu damar shiga shirin sake tinaninsu.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.