Najeriya-MSF

Kungiyar MSF ta fara gangamin tiyata ga masu fama da cutar Noma a Sokoto

Cutar Noma ta fi addabar kananan yara a kasashen da ke yankin kudu da Sahara.
Cutar Noma ta fi addabar kananan yara a kasashen da ke yankin kudu da Sahara. © BMJ

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta MSF da hadin gwiwar ma’aikatar Lafiyar jihar Sokoto ta fara wani aikin tiyatar hadin gwiwa ga kananan yaran da ke fama da cutar Noma a cikin asibitin kula da masu lalurar da ke jihar

Talla

Tun a farkon watan nan tawagar likitocin kungiyar ta MSF suka isa jihar Sokoto, yayinda aka fara aikin a ranar Talata 2 ga watan da muke ciki na Maris, aikin tiyatar da bayar da kulawar da ake saran ya kai har ranar 16 ga wata.

Sanarwar Asibitin ta nuna cewa, yayin makwanni 2 da tawagar likitocin za ta shafa ta na duba masu fama da cutar ta Noma akwai tsarin yin tiyata akalla 19 wadda marasa lafiya 16 za su amfana.

Jagorar shirin na MSF Charity Kamau ta ce wannan ne karon farko da aikin tiyatar karkashin kungiyar likitocin kasa da kasar ke gudana tun bayan bullar annobar Coronavirus da ta durkusar da bangarorin lafiyar kasashe.

A cewarta, tun shekaru 4 da suka gabata gwamnatin Najeriya ke aikin hadin gwiwa tsakaninta da MSF musamman a bangaren da ya shafi tiyatar cutar ta Noma, ta yadda kungiyar ke aiko da tawagar likitoci akalla sau 4 kowacce shekara a wani yunkuri na yakar cutar wadda MSF ke ganin ya dace ace babu burbushinta a ban kasa.

Jagoran shirin a wannan karon, Dr Bukola Oluyide ya ce manufar gangamin tiyatar bai wuce tseretar da kananun yaran daga kyamar da suke fuskanta sakamakon wawakewar wani bangare na naman fuskarsu ba, tare kuma da bayar da shawarwari ga iyaye kan yadda za su kula da yara da nufin yakar cutar wadda karancin sinadaran abinci mai gina jiki da kuma rashin alluran rigakafi ga yara ke haddasawa.  

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.