Najeriya-Sokoto

Sabon farmakin 'yan bindiga ya hallaka mutane 13 a jihar Sokoto

Gawarwakin wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a Zamfara
Gawarwakin wasu mutane da 'yan bindiga suka kashe a Zamfara RFI

Yan bindiga a Najeriya sun kai hari daren jiya a kauyen Tara da ke karamar hukumar Sabon birni, inda suka kashe mutane 13, suka kuma jikkata wasu guda 7.

Talla

Dagacin garin Tara, Mainasara Muhammad Tara ya ce maharan sun yi nasarar kwashe dabbobi da dama, yayin da suka kona rumbunan ajiye abincin su.

Mai garin ya ce 'yan bindigar sun is agarin ne da misalin karfe 11.58 na dare, ta wata barauniyar hanya, saboda gadin da matasa ke yiwa hanyoyin shiga garin.

Muhammad Tara ya ce sun dade basa iya bacci a garin saboda yawan hare haren 'yan bindigar, abinda ya sa suke raba kan su domin sanya ido.

Mai garin ya ce wannan shi ne karo na biyu da 'yan bindigar ke kai musu hari a cikin watanni biyu, kuma a harin farko sun yi asarar dabbobin da yawan su ya kai 200.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.