'Yan bindiga sun kashe mutane 16 a wani sabon hari da suka kai Sokoto

Wasu kauyawa na jana'izar wadanda yan bindiga suka kashe musu a arewa maso gabashin Najeriya a ranar 8 ga watan Janairun 2019
Wasu kauyawa na jana'izar wadanda yan bindiga suka kashe musu a arewa maso gabashin Najeriya a ranar 8 ga watan Janairun 2019 AFP

A Najeriya, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 16 tare da jikkata wasu tara a wani kauye da ke arewa maso yammacin kasar kusa da kan iyaka da jamhuriyar Nijar.

Talla

Harin na Asabar  da aka kai kauyen Tara, dake jihar Sakkwato, shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da '' 'yan bindiga’ 'da suka kwashe shekaru suna addabar jama’a, suna kashe mutane, da kuma yin garkuwa da su domin karban kudin fansa.

Wani mazaunin kauyen mai suna Lawwali Umeh ya ce "'yan bindigar sun zo ne a kan babura inda suka bude wuta a kan mutane."

Umeh ya kara da cewa "Mun binne gawawwaki 16 a yammacin yau. Wasu tara sun samu munanan raunuka."

Wani dan majalisar jiha, Saidu Naino Ibrahim, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu, inda ya ce ana kula da wadanda suka jikkata a asibiti, inda ya kara da cewa "maharan sun tafi da shanu sama da 100".

Dan majalisar ya ce 'yan bindigar sun fito ne daga Dogon Zango, da ga makwabtakansu jihar Zamfara.

Ibrahim ya ce "'yan fashin sun addabi kauyuka a yankin ... suna ta zirga-zirga daga kauye zuwa kauye, suna kashe-kashe da kwace."

Hare-hare na kara ta'azzara a Arewa maso Yammaci

'Yan Bindiga da da ake ganin sun kafa sansanoninsu a dajin Rugu, wanda ya ratsa jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna da Neja na cin karen su babu babba a jihohin.

Duk kuwa da cewa an tura Sojoji yankin tun a 2016, ga kuma yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da wasu 'yan ta'addan a shekarar 2019 amma ana ci gaba da kai hare-hare.

A ranar Talata, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa "yawan tashin hankali a yankin arewa maso yammacin Najeriya ... ya haifar da kwararar jama’a zuwa makwabciyar kasar Nijar".

Tun daga watan Janairu kadai, sama da 'yan gudun hijira 7,660 - galibi mata da yara - suka tsere daga Najeriya zuwa Maradi, in ji UNHCR

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.