Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 11 daga filin jiragen saman Kaduna

Harabar filin jiragen sama da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Harabar filin jiragen sama da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya. © Twitter / @GazetteNGR

Rahotanni daga Kaduna a Najeriya, sun ce ‘yan bindiga sun kutsa kai sashin gidajen ma’aikatan filin jiragen saman jihar, inda suka sace mutane akalla 11, ciki har da iyali guda 6 tare da wata matar aure da ‘ya’yanta 2.

Talla

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar, ‘yan bindigar sun sace mutanen ne da misalin karfe 12 na daren ranar Juma'a wayewar garin Asabar.

Yayin zantawa da manema labarai, wani Injiniya ya ce da fari ‘yan bindigar sun so sace dukkanin mutanen dake zaune a sashin ma’aikatan filin jiragen ne, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, saboda daukin da jami’an tsaro suka kai musu.

Wadanda suka shaida aukuwar lamarin sun ce an shafe tsawon lokaci ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar, kafin daga bisani su tsere.

Kaduna na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga, baya ga Katsina, Zamfara, Sokoto da kuma jihar Neja.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.