Najeriya - Makiyaya

An kashe Fulani makiyaya 4 a jihar Anambra tare da sace musu shanu

Wasu matan kabilun Fulani makiyaya a Najeriya
Wasu matan kabilun Fulani makiyaya a Najeriya AFP

Rahotanni daga jihar Anambara dake Kudu maso Gabashin Najeriya, na cewa, makiyaya hudu aka harbe har lahira a wani hari da aka kai kan matsugunin su dake Ogborji na jihar.

Talla

A cewar Alhaji Gidado Siddiki, Shugaban kungiyar Miyetti Allah (MACBAN), shiyyar Kudu maso Gabas, baya ga kasha makiyayan an kuma sace shanu da yawan gaske  a harin da akai jiya Asabar.

Siddiki ya ce an kashe Fulani makiyaya sama da 20 a Anambra kadai daga watan Janairu zuwa Maris, din da muke ciki.

Fulani makiyaya na cikin fargaba a Najeriya

A Najeriya yanzu haka, Fulani makiyaya na cikin zullumi, a jihohin Oyo da Edo da ke sashen Kudu maso Kudancin kasar da kuma Abiya da Ebonyi a yankin Kudu maso Gabas. 

A yayin da  Kabilun Yarbawa da dangoginsu ke farma Fulani makiyaya  a sassa dabam-dabam a Najeriya, gwamnatin kasar ta ce ta kaddamar da bincike da nufin tabbatar da kariya ga Fulanin da ma daukacin 'yan kasar da ke fuskantar barazana a halin yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.