Najeriya

Wasu shugabannin Yarbawa na ingiza rikici saboda zaben 2023 - Akanbi

Basarake a kasar Yarbawa, Oba AbdulRasheed Akanbi dake Masarautar Iwo yayi zargin cewar wasu shugabannin Yarbawa ne ke kada gangar yaki da zummar haifar da tashin hankali saboda zaben shekarar 2023.
Basarake a kasar Yarbawa, Oba AbdulRasheed Akanbi dake Masarautar Iwo yayi zargin cewar wasu shugabannin Yarbawa ne ke kada gangar yaki da zummar haifar da tashin hankali saboda zaben shekarar 2023. © Daily Trust

Wani Basarake a kasar Yarbawa, Oba AbdulRasheed Akanbi dake Masarautar Iwo yayi zargin cewar wasu shugabannin Yarbawa ne ke kada gangar yaki da zummar haifar da tashin hankali saboda zaben shekarar 2023.

Talla

Sanarwar da Basaraken ya wallafa a shafin sa na Facebook da Jaridar Daily Trust ta wallafa tace duk batun matsalar tsaron da ake ta kambamawa a kudu maso yammcin Najeriya na da nasaba ne da zaben shugaban kasa mai zuwa.

Basaraken yace duk shugabannin Yarbawan dake tinzira tashin hankali a Yankin ba zasu gama da duniya lafiya ba.

Sarki Akanbi yace wadannan shugabannin suna tinzira tashin hankalin ne domin biyan bukatar kan su ta siyasa, musamman masu kada gangar yaki, saboda basa goyan bayan wani dake neman zama shugaban kasa.

Zaben 2023

Basaraken yace wadannan mutane sun san cewar shugaban kasar da za’ayi a Najeriya a shekarar 2023 zai fito ne daga Yankin Yarbawa kuma wadannan mutane basa bukatar ganin haka.

Sarki Akanbi yace ba zasu goyi bayan duk wani mutum dake neman haifar da tashin hankali a Lagos ko kuma lalata Yankin Kudu Maso Yamma ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.