Najeriya-Ilimi

Matsalar tsaro na barazana ga ilimin Mata a arewacin Najeriya

Wasu daga cikin daliban makarantar Jangebe da 'yan bindiga suka taba sacewa a Zamfara.
Wasu daga cikin daliban makarantar Jangebe da 'yan bindiga suka taba sacewa a Zamfara. AP - Sunday Alamba

Hare haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya na cigaba da barazana ga harkar ilimin dalibai musamman mata.

Talla

A karshen watan Fabarairu ‘yan bindiga suka sace dalibai 279 daga makarantar sakandaren ‘yammata ta Jangebe dake jihar Zamfara, wadanda ‘yan bindigar suka saka bayan kwanaki 10.

Dangane da bikin ranar mata ta duniya, Aminu Sani Sado ya hada rahoto kan matsalolin da ke baraza ga ilimi musamman na mata a yankin arewacin Najeriyar.

Rahoto kan yadda matsalar tsaro ke barazana ga ilimin mata a Najeriya
Rahoto kan yadda matsalar tsaro ke barazana ga ilimi mata a Najeriya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.