Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka mutane 937 cikin shekarar 2020 a Kaduna

Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukumomin Najeriya.
Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukumomin Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce 'yan bindiga sun hallaka mutane 937 a shekarar 2020, yayin da suka yi garkuwa da 1972 a kananan hukumomi 23 dake Jihar.

Talla

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan da ke bayyana hakan yayin gabatar da rahoton ayyukan ma’aikatar sa, ya ce an samu kashe-kashen mutane 468 a kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi da giwa da kuma Chikun.

Aruwan ya ce wadannan mutane da aka kashe ko aka yi garkuwa da su sun fito ne daga kabilu da addinai daban daban ba tare da nuna banbanci ba.

Kwamishinan ya ce daga cikin mutane 1,972 da aka yi garkuwa da su, 1,561 sun fito ne daga yankin Kaduna ta Tsakiya, kuma 1,461 daga cikin su an sace su ne a kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi da Giwa da kuma Chikun.

Jami’in wanda ya ce matsalar tsaron ta yi matukar illa ga harkokin noma a wasu yankuna, ya kara da cewar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu na cigaba da zama babbar kalubale wadanda ayyukan su kan haifar da rikici tsakanin al’umma.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai wanda ya jajantawa wadanda matsalar ta shafa, yace gwamnatin sa zata cigaba da taimakawa jami’an tsaro wajen kare lafiyar jama’a da kuma kai hari kan Yan bindigar da ke dazukan Kamuku da Kuyambana.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.