Najeriya-'Yan bindiga

Gwamantin Niger ta kulle dukkan makarantunta saboda rashin tsaro

Dakin karatun makarantar Sakandiren Kagara a jihar Niger da aka sace dalibai cikin watan jiya.
Dakin karatun makarantar Sakandiren Kagara a jihar Niger da aka sace dalibai cikin watan jiya. Kola Sulaimon AFP/File

Gwamnatin Jihar Niger da ke Najeriya ta bada umurnin rufe daukacin makarantun Sakandaren na makwanni biyu saboda abinda ta kira matsalolin tsaron da suka addabe ta.

Talla

Kwamishiniyar ilimi Hajiya Hannatu Jibrin Salihu ta ce daga gobe Juma’a 12 ga watan Maris za’a rufe makarantun zuwa 26 ga wata domin bai wa hukumomin tsaron jihar sake dabaru domin inganta tsaron lafiyar dalibai da malaman su.

Lokacin hutun zai bada damar duba hanyoyi daban daban da za’a inganta harkar tsaron da gine gine makarantun da kuma samar da kayan aiki tare da nazari kan irin rawan da shugabannin makarantun da kuma malamai zasu taka.

Jihar Niger sannu a hankali na zama dandalin Yan bindigar dake kai hare hare makarantu, ganin yadda suka kwashe dalibai 27 da malamai guda 3 da iyalan su 12 a makarantar Sakandaren kagara, bayan sun harbe daya daga cikin daliban Benjamin Doma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.