Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta koka kan karancin kudi

Wani sashin ginin zauren majalisar dokokin Najeriya dake birnin Abuja.
Wani sashin ginin zauren majalisar dokokin Najeriya dake birnin Abuja. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar Wakilan Najeriya tace ta talauce yadda ba za ta iya gudanar da wasu ayyukan da suka rataya akan ta ba saboda karancin kudade.

Talla

Mai Magana da yawun Majalisar, Benjamin Kalu daga Jihar Abia ya bukaci karawa Majalisar kudaden da ake ba ta a kasafin kudi daga naira biliyan 128 da aka bata a wannan shekarar.

A cewar Kalu, ya dace ‘Yan Najeriya su fahimci cewar kudaden da aka ba ta a kasafin kudin wannan shekarar da aka yi akan naira 180 kowanne Dala guda ya gaza, ganin yadda yanzu ake sayar da Dalar akan naira 400.

Matsalar da karancin kudi ya haifar

Kakakin Majalisar ya ce wannan ya sa dole suka jingine wasu ayyukan da suka rataya akan su saboda karancin kudi.

Yan Najeriya da dama na kallon Majalisar dokokin kasar a matsayin inda ake kashe makudan kudade sabanin wasu fannoni da suke ganin ya dace a mayar da hankali akai.

Sai dai duk da korafin da jama’ar kasar da dama ke yi, Majalisar dokokin taki amincewa da bukatar rage albashin ma’aikatan ta da kuma wakilan da suka fito daga jihohi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.