Najeriya-Hakkin dan Adam

NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan makomar albashin ma'aikata

Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya yayin zanga-zanga a birnin Abuja.
Wasu 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya yayin zanga-zanga a birnin Abuja. ASSOCIATED PRESS - SUNDAY ALAMBA

A Najeriya kuwa kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta yi gargadin barazanar tafiya yajin aiki, matukar majalisun tarayyar kasar ba su janye kudurin su na sake nazaratar dokar mafi karancin albashi na kasar ba.

Talla

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ke jawabi gaban daruruwan mambobin kungiyar da suka gudanar da wani tattaki zuwa zauren majalisar.

Wabba ya kuma kwatanta yunkurin zare dokar mafi karancin albashin daga cikin jadawalin dokokin majalisar a matsayin daura damarar yaki da kungiyar kwadagon.

Matukar dai wannan yunkuri na majalisar ya yiwu, to za a baiwa gwamnonin jihohi damar biyan ma’aikatan su abinda suka ga dama a matsayin albashi, ba tare da la’akari da tsarin gwamnatin tarayyar kasar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.