Najeriya - Buhari

Bidiyo: Buhari ya bukaci harbe duk wanda aka samu dauke da AK 47

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin wani taro a fadar sa ta Asorok
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin wani taro a fadar sa ta Asorok © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurmin harbe duk wani da aka samu dauke da bindiga kirar AK 47 a cikin dazukan kasar, makamin da ake ganin 'yan bindiga da kuma mayaka masu ikirarin jihadi, masamman Boko Haram ke amfani da shi.

Talla

A baya bayan nan dai matsalar tsaro ta hare-haren 'yan bindiga ta yi kamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya dauki sabon salo ta yadda barayin suka maida hankali kan kaiwa makarantu farmaki, tare da sace daruruwan dalibai, wadanda daga bisani suka saki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.