Najeriya-Jos

Kotun Koli ta tabbatar da daurin shekaru 10 kan tsohon Gwamnan Filato

Tsohon gwamnan jihar Filato dake Najeriya Joshua Dariya.
Tsohon gwamnan jihar Filato dake Najeriya Joshua Dariya. © International Centre For Investigative Reporting

Kotun Kolin Najeriya yau ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 10 da ta yiwa tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Joshua Dariye saboda samun sa da laifin zamba cikin aminci, yayin da ta wanke shi daga tuhumar kashe naira biliyan 2 ta hanyar da basu kamata ba.

Talla

An tuhumi tsohon Gwamnan ne da laifin barnatar da naira biliyan 2 lokacin da ya mulki Jihar Plateau a wa‘adin sa na farko tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, abinda ya sa kotu ta same shi da laifi a shekarar 2018 ta kuma daure shi a daidai lokacin da yake rike da mukamain Sanata mai wakiltar Plateau ta Tsakiya.

Mai shari’a Adebukola Banjoko na Babbar kotun Abuja ya fara daure tsohon Gwamna Dariye shekaru 14 ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2018 kan tuhumar da aka masa, kafin kotun daukaka kara ta rage shekaru zuwa 10 ranar 16 ga watan Nuwambar shekarar 2018.

Yayin yanke hukunci yau kan korafin da tsohon Gwamnan ya gabatar domin sake nazarin hukuncin, mai shari’a Mary Odili da ta jagoranci tawagar alkalai guda 5 ta sanar da soke hukuncin daurin da aka masa kan kashe kudade ta hanyar da basu kamata ba mai dauke da hukuncin daurin shekaru 2, yayin da alkalan guda 5 suka tabbatar da hukuncin daurin shekaru 10 kan laifin zamba cikin aminci.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.