An nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a matsayin Jagoran Tijjaniya

Tsohon Sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi II
Tsohon Sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi II REUTERS/Akintunde Akinleye

Mabiya darikar Tijjaniya a Najeriya sun nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu a matsayin jagoran su domin maye gurbin marigayi Sheikh Khalifa Isyaku Rabiu da ya rasu a shekarar 2018.

Talla

An bayyana nadin Sanusi na Biyu ne a wani gagarumin taron mabiya darikar da ya samu halartar dubun dubatan mutane a birnin Sokoto cikin su harda Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Wannan nadi na zuwa ne shekara guda da sauke Muhammadu Sanusi na Biyu da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi daga karagar mulkin Sarautar Kano.

Kakan tsohon Sarkin ya taba rike wannan mukami na jagoranci mabiya darikar Tijjaniya a Najeriya.

Ita dai wannan darika ta Tijjaniya da ta samo assali daga Yankin arewacin Afirka ta yadu sosai a Yankin Afirka ta Yamma musamman a kasashe irin su Senegal da Gambia da Mauritania da Mali da Guinea da Jamhuriyar Nijar da Chadi da Ghana da Najeriya da kuma Sudan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.