Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya 19 da Yan sa kai 4

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi Guardian Nigeria

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe sojojin gwamnatin Najeriya 19 da Yan sakai 4 a wani harin kwantar baunar da suka musu a Gudumbali dake kusa da Tafkin Chadi.

Talla

Wannan hari na daga cikin na baya bayan nan a rikicin da yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 36,000 da raba daruruwan mutane da matsugunan su bayan kwashe sama da shekaru 10 ana fafatawa.

Wata majiyar soji ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa mutuwar sojojin sakamakon harin, yayin da wasu 10 suka samu raunuka.

Majiyar tace sun gamu da kwantar baunar ce lokacin da tawagar motocin su guda 10 ke tafiya tsakanin Kukawa zuwa Gudumbali.

Rahotanni sun ce an kawo wadanda harin ya ritsa da su zuwa birnin Maiduguri, kuma daga cikin wadanda suka mutu a bangaren Yan Sakai harda Umar Ari.

Kungiyar ISWAP ta sanar da kai harin wanda tace yayi sanadiyar kashe jami’an tsaro 33 da jikkata wasu kusan 20, yayin da suka dauki guda a matsayin firsina.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.