Najeriya-Kaduna

Yan bindigar da suka sace daliban Kaduna sun bukaci naira miliyan 500

Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga.
Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga. © PHOTO/FOTOSEARCH

Yan bindigar da suka sace daliban kwalejin jihar Kaduna dake Najeriya sun saki bidiyon dake dauke da daliban inda suke bukatar biyan su diyyar naira miliyan 500 kafin su sake su.

Talla

Wasu daga cikin iyayen yaran dake kwalejin sun gane yaran su dake cikin bidiyon kamar yadda suka shaidawa Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Abuja.

Wasu daga cikin daliban da suka yi magana a bidiyon wanda ke nuna Yan bindigar dauke da bindigogi sun bukaci gwamnati da ta taimaka wajen kubutar da su ba tare da amfani da karfi ba.

A bidiyo na biyu an ga Yan bindigar na dukan daliban da bulala suna ihu, inda suke bayyana cewar rayuwar su na cikin hadari.

Daya daga cikin daliban yace da yawa daga cikin su sun samu raunuka, kuma lokaci na kurewa, yayin da wasu daga cikin su ke fama da matsalolin rashin lafiya.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta wallafa Bidiyon da 'Yan bindiga suka yada dake nuna Daliban da suka sace.

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.