Najeriya-Kaduna-'Yan bindiga

An ceto dalibai fiye da 300 daga shiga hannun 'yan bindiga a Kaduna

Misali na 'yan bindiga da suka addabi sassan arewacin Najeriya.
Misali na 'yan bindiga da suka addabi sassan arewacin Najeriya. Solacebase

‘Yan bindiga sun sake yin yunkurin sace mutane a karo na biyu a rukunin gidajen ma’aikatan filin tashi da saukar jiragen sama na Kaduna a arewacin Najeriya.

Talla

Sun kutsa makarantar ne da sanyi safiyar Lahadin nan, amma kuma sojoji suka bata shirinsu na yin awon gaba da dalibanta, a cewar kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.

Aruwan ya bada tabbacin cewa dukkannin dalibai 307 na makarantar su na nan.

Wannan  lamari na zuwa  ne kwanaki 2 bayan da wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan kwalejin nazarin ayyukan gandun daji da ke Afaka,  karamar hukumar Igabi ta jihar Kadunar.

Karo  na 3 kenan da dakarun sojin kasar ke samun nasarar dakile shirin satar mutane  a Kaduna a cikin sa’o’i 48.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.