Najeriya-Atiku

Atiku ya bukaci 'yan Najeriya su daina biyan kudin fansa ga 'yan bindiga

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar.
Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar. REUTERS/Tife Owolabi

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bukaci 'yan kasar su dai na biyan diyya idan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kwashi 'yan uwansu, inda ya ke cewa matakin na wucin gadi ne wanda zai haifar da matukar illa nan gaba.

Talla

Yayin da ya ke tsokaci kan sace wasu karin dalibai da malaman su da 'yan bindiga suka yi a Kaduna, Atiku ya sake kira ga gwamnatin Najeriya da ta kafa dokar ta baci kan harkar ilimi wanda zai bada damar samar da tsaro na sa’oi 24 akan kowacce makarantar dake yankin da ake fama da wannan matsala da jihohin dake makotaka da su.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya bayyana Najeriya a matsayin Cibiyar Duniya da ake fama da yaran da basa zuwa makaranta sakamakon samun yara sama da miliyan 13 da rabi, ya ce wadannan hare hare da ake kai wa makarantu za su dada ta’azzara matsalar.

Atiku ya ce ya zama wajibi a matsayin mu na kasa mu dauki kwararan matakai domin kawo karshen wannan sankarar satar dalibai a makarantu da kuma samar da manufofin da zasu kare daliban.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.