Najeriya- Maiduguri

Daruruwan mata na zanga zanga kan bacewar 'ya'yansu a Maiduguri

Wasu dandazon mata da suka rasa matsugunansu a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Wasu dandazon mata da suka rasa matsugunansu a birnin Maiduguri na jihar Borno. AFP PHOTO/STRINGER

A garin Maiduguri da ke jihar Bornon Najeriya, daruruwan iyaye mata da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin mata da yara kananan ne suka shirya zanga-zangar lumana jiya lahadi domin neman bayanai kan ‘ya‘yan su da suka ce jami’an tsaron sun kame sama da shekaru 10 kuma babu labarin su har yanzu. Wakilinmu a Maidugri Bilyamin Yusuf, ya hada mana wannan rahoto.