Najeriya-Ngozi

Goyan bayan da Buhari ya bani ne ya taimaka min samun nasara - Ngozi

Shugabar hukumar kasuwanci ta Duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala.
Shugabar hukumar kasuwanci ta Duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala. AFP/Archivos

Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya Ngozi Okonjo-Iwela ta ce taimako da goyon bayan da shugaban kasarta Najeriya Muhammadu Buhari ya yi mata ne ya bata damar samun nasarar hawa kujerar jagorancin hukumar ta WTO.

Talla

Yayinda ta kai masa ziyarar godiya a fadar sa, Ngozi Okonjo-Iweala ta ce zabin da kayi mani wajen tsayawa takara da daruruwan wasikun da ka rubutawa shugabannin duniya da kiran da kayi musu ta waya domin goya min baya sun taimaka min wajen samun nasara.

Shugabar hukumar ta ce da badan goyan bayan da shugaba Buhari ya bata ba, da zai yi wuya ta hau kujerar da take kai ayau.

A nashi jawabi, shugaba Buhari ya ce duk da goyan bayan da gwamnatin sa ta bata, Ngozi Okonjo-Iweala na da kwarewar da ake bukata na jagorancin hukumar.

Buhari ya ta ya Okonjo-Iwela murna tare da yi mata fatar alheri wajen sauke nauyin da ke kan ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.