Najeriya-Boko Haram

Sojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 31 tare da ceto mutane 60

Wasu Sojin Najeriya bayan nasara kan mayakan Boko Haram a Maiduguri.
Wasu Sojin Najeriya bayan nasara kan mayakan Boko Haram a Maiduguri. AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da hallaka mayakan boko haram 31 da kuma ceto mutane 60 da suka yi garkuwa da su a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da hare-haren ta'addancin kungiyar.

Talla

Sanarwar da Daraktan yada labaran hukumar Janar Mohammed Yarima ya rabawa manema labarai tace sojojin a karkashin rundunar Zaman Lafiya Dole sun yi arangamar ne akan hanyar Gulwa zuwa Musuri dake Gamborou Ngala a Jihar Barno.

Sanarwar ta ce sojojin sun kwashi akalla mintina 45 suna fafatawa da mayakan abinda ya basu nasarar hallaka 31 daga cikin su, da kuma samun tarin makamai daga hannun su.

Daga cikin mutanen da aka kubutar a hannun mayakan harda wasu dattijai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.