Najeriya-Kaduna

El Rufa'i ya jaddada matsayar sa ta kin tattaunawa da 'yan bindiga

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i Twitter@GovKaduna

Gwamnan Jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasir El Rufai ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na kin tattaunawa da Yan bindiga domin biyan su kudin diyya kan daliban da suka sace.

Talla

El Rufai yace ko sisin kwabo gwamnatin Jihar Kaduna ba za ta biya Yan bindigar ba wadanda suke rike da dalibai 39 da suka sace a makon jiya.

Gwamnan yace matsayin su na gwamnati shine matsayin gaskiya, domin sun yi nasarin halin da ake ciki, kuma basu ga wani dalili da zai sa gwamnati zata biya kudi ga Yan bindiga domin sayen manyan makamai suna amfani da su wajen kai munanan hare hare akan al’umma  ba.

El Rufai yace wannan manufar gwamnati ce, cewar baza su biya diyya ba kuma ba zasu tattauna da masu aikata laifi ba ko kuma bindiga ba.

Daliban kwalejin ayyukan Gandun Daji na cikin koshin lafiya

Gwamnan yace mallakar bindiga kirar AK47 ba zai baka damar tattauna da gwamnati ba, domin idan sun yi haka toh zamu cigaba da tattaunawa da duk wani mai aikata laifi a Najeriya, da kuma gabatar masa da afuwa, wanda hakan ba zai taimakawa Jihar Kaduna da kuma Najeriya ba.

El Rufai ya tabbatar da cewar daliban su 39 na Babbar kwalejin Gandun Daji na hannun Yan bindigar da suka sace su, kuma sun san suna cikin koshin lafiya, saboda dakarun Najeriya na kai shawagi inda ake tsare da su.

Gwamnan yace sun bayyana musu karara cewar ko kwabo ba zai je wurin su daga asusun gwamnatin jihar Kaduna ba, kuma suna jira da fatar ganin an sako su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.