Najeriya-Ilimi-Garkuwa da mutane

Garkuwa da dalibai na yi wa ilimi barazana a arewacin Najeriya - Tofa

'Yan matan makarantar sakandaren  Dapchi da aka fansa daga hannun Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya tare da shugaban kasar Muhammadu Buhari.
'Yan matan makarantar sakandaren Dapchi da aka fansa daga hannun Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya tare da shugaban kasar Muhammadu Buhari. Nigeria Presidency/Handout via Reuters

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a Najeriya sun bayyana ci gaba da kai hari makarantu ana kwashe dalibai da malamai a matsayin wani shiri da zai durkusar da harkar bada ilimi a arewacin kasar baki daya.

Talla

Masanan sun ce yayin da hare haren boko haram suka fi ta’azzara a yankin arewa maso gabas, hare haren yan bindiga sun fadada zuwa akasarin jihohin da ke yankin arewa maso yamma da kuma jihohin Nasarawa da Benue da Kogi da Plateau da birnin Abuja.

Tun bayan kwashe daliban makarantar sakandaren Chibok 276 da aka yi a shekarar 2014, an samu karuwar matsalar wadda ta hada da ta Dapchi a shekarar 2018 wanda aka kwashe dalibai 113, sai kuma Kankara a shekarar nan,  inda aka kwashe dalibai 344.

A wannan shekara ta 2021 'yan bindigar sun kwashe dalibai 27 a Kagara, 317 a Jangebe, 39 a Mando, sai kuma dalibai 3 da malamai 3 a makarantar Firamaren Rama dake Jihar Kaduna.

Tsohon dan takaran shugaban kasar Najeriya Alhaji Bashir Othman Tofa ya bayyana lamarin wanda ya kai ga rufe makarantu a wasu Jihohi a matsayin abin takaicin da ya afkawa arewacin Najeriya.

Tofa ya ce kungiyar Boko Haram da masu daukar nauyin su da kuma masu goya musu baya zasu bayyana farin cikinsu da lamarin wanda ya kai ga rufe makarantun da kuma biyan diyya ga 'yan bindigar da ke garkuwa da mutane.

Tsohon dan takaran ya ce wannan matsalar zai haifar da gagarumar koma baya wajen harkar bada ilimi a yankunan da ake fama da talauci da kuma jahilci, yayin da ya bayyana cewar makiyan arewacin kasar za su yi ta dariya, ba tare da sanin cewar matsalar da ke ci kamar wutar daji na iya cim musu ba, domin kuma babu ruwan aikata laifuffuka da kabila ko addini.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.