Wasanni - Ingila

Guardiola ya ce babu sabani tsakaninsa da Sterling

Kocin manchester City, Pep Guardiola.
Kocin manchester City, Pep Guardiola. Martin Rickett POOL/AFP

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya yi watsi da batun cewa akwai sabani a tsakaninsa da dan wasan kungiyar, Raheem Sterling, inda ya ce ba wani sabon abu bane dan wasa ya nuna rashin jin dadi idan ba ya cikin tawagar da za ta fafata a wasa.

Talla

Abin ya zo da mamaki da ba a ga Sterling a wasan  City da Fulham ba, kana ya yi zaman benchi har karshen wasan da suka doke Southampton kwanaki 3 a tsakani.

Dan wasan tawagar kasar Ingila din ya yi tattaki da City zuwa Borussia Monchengladbach don wasan zakarun nahiyar Turai a Talatar nan, kuma Guardiola ya ce babu wata matsala a tsakaninsu.

Amma ya kara da cewa a cikin shekaru 40 da ya yi a sana’ar kwallon kafa, bai taba ganin ko da dan wasa daya da ya ji dadin rashin damawa da shi a wasa ba, ko da kuwa ba shi da lafiya ne, saboda haka ba wani bakon abu ba ne idan Sterling ya nuna rashin jin dadi.

Sterling ya fafata wa City  a wasanni 36 a  dukkannin gasanni a wannan kaka, kuma kwallaye 14 ya saka a raga.

Kafin yanzu ya jefa kwallaye   5 a raga a cikin wasanni 6 a cikin watan Janairu zuwa Fabrairu, amma sai daga bisani ya jera wasanni 3 ba tare da cin kwallo ko da guda ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.